Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici ya raba jam'iyyar PDP gida biyu a jihar Adamawa


PDP
PDP

Wata sabuwar badakala ta kunno kai a jam'iyyar PDP game da zaben matakin anguwanni a jihar Adamawa lamarin da ya sa ta rabe gida biyu.

Wannan darewar ta biyo bayan rikicin da wasu shugabannin jam'iyyar suka shiga akan zargin cewa wasunsu sun yi awan gaba da kayan zabe da aka turo jihar.

Yayinda yake karban malaman zaben da uwar jam'iyyar ta turo jihar domin gudanar da zabukan shugaban jam'iyyar a jihar Chief Jonah Joel Madakai ya nuna bacin ransu ne tare da zargin cewa tsohon hadimin shugaban kasa Goodluck Jonathan wato Barrister Ali Gulak shi ya yi awan gaba da kayan zaben.

Amma Barrister Ali Gulak ya musanta zargin. Yace uwar jam'iyyar ta bukaci a biyata nera miliyan tara kafin ta aika da kayan zaben amma shi ya shaidawa shugaban jam'iyyar cewa mutanensu ba zasu iya fitar da kudin ba nan take. Ya roka a bada kayan bayan an sayar sai a maida masu kudin. Dalili ke da uwar jam'iyyar tace idan zai dauki alkawarin biyan kudin ya rubuta masu su bashi kayan. Haka ko ya yi.

Yace da aka bashi takardun zaben sai ya mikawa wadanda jam'iyyar zata aika Adamawa su gudanar da zaben. Bayan awa uku Joel Madaki ya je neman kayan aka yi masa bayanin abun da ya faru.

Shugaban tawagar jami'an zaben yace zasu gudanar da zabukan tun daga matakin anguwanni har zuwa jiha, sai sun gama kakaf tsakininsu da Allah.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG