Dokar Ta Baci Najeriya

Sojojin Najeriya, Mayu 16 2013

Kwana guda bayan da shugaban Nigeria ya ayyana dokar ta baci a jihohi uku na Arewa maso gabashin Nigeria, jami’an tsaro, sun karfafa daukan matakan ganin an dakile ayyukan ta’addanci ta hanyar kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan da ‘yan tsagera suka ja daga.

Rundunar sojin Nigeria ta fidda wata sanarwar dake dauke da bayanin cewa jami’an soja sun fara kakkabe da rairaya a yankunan kan iyakokin Nigeria inda ‘yan tsagerar keda sansanoninsu. A nan birnin Washington, D.C. na Amurka kuma, ma’aikatar harkokin waje ta tayi kira ne ga hukumomin Nigeria da su tafi sannu a hankali a rika kulawa da hakkin Bil Adama a lokacin da ake bin diddigin ‘yan ta’adda. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Patrick Ventrell yayi bayanin matsayin Amurka game da daukan matakan dakile ‘yan ta’adar da Nigeria yanzu keyi inda yake cerwa,Amurka na yin kira ga jami’an Nigeria da a tabbatar da cewa matakan tsaron da jami’ai ke dauka domin Dakile ayyukan ta’addanci,an daukesu cikin nutsuwa tare da yin la’akkari da hakkin Bil Adama, a rika kulawa da yin kakkaben cikin adalci da bin dokokin kasa da kasa dangane da kare mutumcin Bil Adama.