Yawaitar hare-hare da sace mutane da ake yi a kan hanyoyin Birnin Gwari, ya sa kungiyar direbobi masu zaman kansu wato NURTW duba yiwuwar dakatar da zirga-zirga a hanyoyin domin kare lafiyarsu.
Shugaban kungiyar na gefen arewa maso yammacin Najeriya, Alhaji Haruna 313 ya bayyana cewa, ba su san adadin jama'ar da aka sace kan hanyoyin ba, domin kusan kullum tsakanin Birnin Gwari zuwa Funtua sai an sace mutum. Abin har ya kai ga mutane suna daukar hanyar Kaduna don zuwa Dandume domin neman a tsira, a cewarsa.
"Sai dai yanzu wannan hanyar Kadunan ma sun dawo sun rufe, ba dare ba rana, a koda yaushe sai dai a kiramu a waya, a ce an dauki mutum biyu, biyar - wata motar bas mai mutum goma 18 in ta zo a cike, sai duk a saukesu a korasu a je kuma ana neman kudin fansa," inji shugaban
Ga wadannan direbobin, abu ya kai makura, dole su dakata har sai abubuwa sun inganta.
Hanyar birnin Gwari ya zama tarkon mutuwa ganin yadda ake yawan sace mutane da kuma hare-haren da ake kai wa yankunan Birnin Gwari wanda har manyan hafsoshin tsaro ke kai ziyara da ikirarin kawo karshe wadannan tashe-tashen hankali.
Saurari cikakken rohoton Isah Lawal Ikara
Your browser doesn’t support HTML5