Kayayyakin da hukumar ta kama sun hada da buhunan shinkafa da motoci na alfarma da kudadensu yah aura biliyoyin Nera. Hukumar ta gargadi ‘yan sumoga da su guji yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa.
Muhammad Uba shugaban kwastan dake kula da shiyar yammacin Najeriya ya shedawa Muryar Amurka
cewar kayayyakin da suka kama sun hada da motoci da tsoffin tayoyi da buhun shinkafa 5516 da aka kiyasta kudinta akan Nera miliyan 76.5. Amma duk da haka kwantrolan y ace shigo da shinkafa ya ragu ainun.
Wannan kamun ya zo ne a makon da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana cewa gwamnati ta daina shigo da shinkafa daga kasashen ketare.
Alhaji Musa Maitakobi ya goyi bayan dukufa da gawamnati akan noma. A cewarsa babu wata fasaha da mutum zai nema idan yanajin yunwa. Kasashe kamar su China, Thailand da Brazil da makamantansu da noma suka fara.
Ga rahoton Banagida Jibrin da karin bayani
Facebook Forum