Babbar kotun jihar Filato ta umurci a ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Jonah Jang a kurkuku har zuwa ranar 24 ga wannan watan lokacin da zata saurari batun neman belinsa.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ko EFCC ita ce ta shigar da kara tana zargin tsohon gwamnan da yin sama da fadi da zunzurutun kudi har Nera biliyan shida da miliyan dubu uku.
Alkalin kotun Daniel Longji ya ki amincewa da bukatar belin tsohon gwamnan, wato zai kasance da zaman kurkuku har zuwa mako mai zuwa ranar 24 ga wannan watan.
Jami'an tsaro sun dauki tsauraran matakan tsaro a hanyar shiga kotun jiya lokacin da aka gurfanar da tsohon gwamnan.
Hukumar EFCC tana tuhumar Jonah Jang da wawure Nera 6.3bn daga cikin tuhume-tuhume 12 da take yi masa da suka hada da almubzaranci da karkata kudin jama'a, cin amana da rashin gaskiya amma ya musanta dukansu.
Alkalin kotun ya ki amincewa da bada belin tsohon gwamnan sai ya yi nazari akai.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani
Facebook Forum