Sifeta Janar na ‘yan sanda Najeriya, Ibrahim Idris, ya ba da umurnin cire kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kogi, CP Ali Janga.
Ya ba da umurnin ne bayan yin nazari kan yadda aka yi sakaci aka bari wasu mutane shida suka gudu daga hannun 'yan sanda, ciki har da mutane biyu da suka zargi Sanata Dino Melaye da saya masu makamai.
Mutane biyun sun hada da Kabiru Seidu wanda aka fi sani da “Osama” da Nuhu Salisu, wanda ake wa lakabi da “Small.”
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin ‘yan sanda jihar ta Kogi, dauke da sa hannun Kakakin ‘yan sanda jihar, ACP Jimoh Moshood, ta ce “CP Esa Sunday Ogbu, wanda kwamishinan ‘yan sanda ne a hedkwata a Abuja, ya karbi mukamin kwamishinan na ‘yan sadan jihar Kogi ba da bata lokaci ba.”
Baya ga haka, yanzu haka, ana tsare da jami’an ‘yan sanda 13 da ake zargi na da hannu a tserewar mutanen.
'Yan sanda Na Neman Dino Melaye Ruwa a Jallo
Gabanin cire kwamishinan 'yan sandan na jihar Kogi, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ayyana Sanata Dino Melaye a matsayin mutumin da take nema ruwa a jallo.
Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa ‘yan sandan na neman Sanata Melaye, wanda ke wakiltar mazabar Kogi ta Yamma a majalisar Dattawa, tare da wasu mutane shida da ake zargi da aikata laifi a jihar Kogi.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, ‘yan sandan sun bayyana cewa daga cikin mutanen da suka gudu har da wasu mutum biyu da aka kama da makamai wadanda suka bayyana cewa Melaye ne ya ke saya masu makaman.
A makon da ya gabata, ‘yan sandan jihar ta Kogi suka fito da Kabiru Seidu da Nuhu Salisu baina jama’a, inda suka sanar da cewa an kama su da makamai.
‘Yan sandan sun kuma bayyana cewa mutanen sun ce Sanata Dino Melaye ne ya ke ba su kudaden sayen makaman.