Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (World Food Program ) ta ce za ta dakatar da aikinta a kasar Chadi inda ake tsugune da kusan ‘yan gudun hijira miliyan daya da suka nemi mafaka a kasar bayan tserewa rikicin kasar Sudan.
Daga cikin ‘yan gudun hijirar akwai daruruwan ‘yan Najeriya da suka makale amma ke yin kira ga gwamnatin kasar don ganin an mayar da su gida.
Daga cikin fargabar da aka bayyana tun bayan barkewar rikicin na Sudan a watan Afrilun wannan shekarar ta 2023 sun hadar da yunwa da karuwar ‘yan gudun hijira.
Yanzu haka dai, hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayana cewa, nań da watan Janairun 2024 mai zuwa za ta dakatar da aikinta a yankin saboda matsalar karancin kudi a yayin da kungiyar MSF ta Doctors Without Borders ta yi karin haske kan manyan kalubalen da aikinta ke fuskanta ta bakin mai magana da yawunta a yankin na Adre Stephanie Hoffman
Tace, "A farkon watan Nuwamba ‘yan gudun hijira fiye da dubu goma ne suka isa kasar Chadi daga Sudan, babbar matsalar yanzu ita ce, barkewar tamowa a sansanin ‘yan gudun hijirar a daidai lokacin da hukumar samar da abinci ta Duniya ke barazanar dakatar da aikinta saboda karancin kudi nan da sabuwar shekara mai zuwa, saboda haka muna cikin fargaba kan abin da ka iya biyo baya da zarar aka dakatar da aikin samar da abincin’’
Daga bisani kuma Mohammed Saleh Iliyasu, Sarkin Hausawa na garin Ader, ya yi kira ga gwamnatin Najeriyar da ta dauki matakin kawo masu taimakon gaggawa.
Masu sharhi na ganin rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya da na Gabashin Turai sun ci gaba da daukar hankalin duniya ba tare da an bada karfi don ganin an shawo kan rikicin na Sudan ba.
Saurari rahoton Ramatu Garba:
Your browser doesn’t support HTML5