Dillalai Na Shafe Kwanaki A Matatar Dangote Kafin A Yi Musu Lodin Fetur - IPMAN

Tallafin Mai A Najeriya Ya Haura Dala Biliyan 1 A Watan Agusta Yayin Da Take Kara Samar Da Man Fetur

Garima ya bayyana mamaki yadda mamallakin matatar man Dangote yace dillalan man na kauracewa matatarsa ta hanyar shigo da fetur din daga ketare.

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta (IPMAN) tace mambobinta basa iya lodin fetur daga matatar Dangote dake Legas duk da cewar sun biya kamfanin man Najeriya (NNPCL) Naira biliyan 40.

Shugaban IPMAN Abubakar Garima ne ya bayyana hakan a shirin hantsi na tashar talabijin ta channels “Sunrise Daily” na yau Laraba.

Garima ya bayyana mamaki yadda mamallakin matatar da aka kashe dala bilyan 20 wajen kafawa Aliko Dangote yace dillalan man na kauracewa matatarsa ta hanyar shigo da fetur din daga ketare.

Shugaban IPMAN din yace mambobinsa basa shigo da fetur daga ketare, sabanin ikirarin da Dangote ya yi.

Ya kara da cewar a maimakon samun man daga matatar Dangote ta hanyar NNPCL, kamata yayi matatun mai masu zamn kansu su yiwa dillalan rijista kai tsaye domin lodin albarkatun man ba tare da wata matsala ba.

A jiya Laraba ne shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bukaci kamfanin man Najeriya (NNPCL) da dillalan man dake fadin kasar su dakata da shigo da man daga ketare, da yake jawabi ga manema labaran fadar gwamnatin Najeriya a Abuja.

Aliko Dangote

Ya kuma bayyana fatan cewar matatar mansa ce za ta warware matsalar layukan ababen hawa a gidajen man dake fadin Najeriya.

“Ina sa ran NNPCL da dillalan mai zasu daina shigo da man daga ketare, kamata yayi su zo su karbi abinda suke bukata. Matukar suka zo suka karba ba za’a sake ganin layukan mai a gidajen man Najeriya ba”, a ccewarsa.