Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Tabbatar Da Sabbin Ministoci


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

A ranar 24 ga watan Oktoban da muke ciki ne Majalisar Dattawan ta karbi bukatar neman tabbatar da nadin sabbin ministoci da ya tura sunayensu .

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da ministoci 7 da Shugaban kasar Bola Tinubu ya aika mata.

Ministocin da aka tabbatar sun hada da Nentawe Yilwatda ta ma’aikatar jin kai da rage talauci, da Muhammad Maigari Dingyadi na ma’aikatar kwadago da ayyukan yi da, Bianca Odumegwu-Ojukwu karamar minista a ma’aikatar kasashen waje da kuma Jumoke Oduwole ta ma’aikatar masana’antu, ciniki da zuba jari.

Sabbin Ministoci
Sabbin Ministoci

Sauran sun hada da Idi Mukhtar Maiha na ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi, da Yusuf Ata, karamin minista a ma’aikatar gidaje da raya birane sai kuma Suwaiba Ahmad, karamar ministar ilimi.

A makon jiya ne Tinubu ya sallami ministar harkokin mata, Uju-Ken Ohanenye da ta yawon bude ido; Lola Ade-John da ministan ilimi, Tahir Mamman da karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Gwarzo da kuma Jamila Ibrahim, ministar ci gaban matasa.

Ya kuma sauyawa 10 wurin aiki sannan ya mika sunayen sabbin ministoci 7 din da zai nada ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da tabbatarwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG