Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Dakatar Da Babban Bankin Najeriya Daga Sakin Kason Kudade Ga Gwamnatin Ribas


Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Siminalayi Fubara (Facebook/Fubara)
Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Siminalayi Fubara (Facebook/Fubara)

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta babbar kotun tarayya dake Abuja ta dakatar da Babban Bankin Najeriya daga cigaba da sakin kason kudaden wata-wata ga gwamnatin jihar Ribas.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik tace ci gaba da karba da rarraba kason wata-watan da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ke yi ya sabawa kundin tsarin mulki kuma bai kamata a bari ta ci gaba ba.

Alkalin ta cigaba da cewar gabatar da kasafin kudin 2024 da Gwamna Fubara ya yi a gaban majalisa mai wakilai 4 sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki ne.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta kara da cewa abinda gwamnan ya aikata ya yi mummunan cin karo da kundin tsarin mulkin 1999.

A karshe dai alkalin ta dakatar da babban bankin najeriya da babban akanta na tarayya da bankunan Zenith da Access daga cigaba da barin Fubara ya taba kudaden dake cikin asusun tarayya dana tara kudaden shigar gwamnati.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG