Mai tsaron raga na Manchester United, David de Gea na shirin kasancewa mai tsaron ragar da yafi kowane daukanr albashi a duniyar kwallon Kafa bisa yarjejeniyar sabon kwantirakinsa a kungiyar ta Manchester United, wadda aka cimma yarjejeniya tun a farkon wata, inda zai karbi zunzurutun kudi har yuro miliyan 21 a tsawan shekaru 5 da zai kwashe yana aiki a kungiyar.
Kasancewar mai tsaron raga Manuel Neuer, ne kawai yake karbar yuro miliyan 15 a kungiyar Bayern Munich.
A bayan gasar cin kofin duniya na bana zai rattaba hanu a sabon kwantirakin.
Dan wasan tsakiya na Chelsea Eden Hazard, ya aika wa kungiyar ta Chelsea, da sakon gargadi domin sanin matsayin sa ko kuma shida da kansa yayi la'akari da abinda yaga ya dace masa ganin kungiyar Real madrid tana sha'awar daukan dan wasan da ya dawo gareta.
Manchester City, tana dab da kammala yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiya na kungiyar Napoli Jorginho, dan shekaru 26, da haihuwa akan kudi fam miliyan £46.5
Everton tana zawarcin dan wasan gefe na Supporting Lisbon Gelson Martins, mai shekaru 23, a duniya da kuma dan wasan baya daga Ajax Matthijs De Ligt, dan shekaru 18 da haihuwa.
Liverpool tana bukatar kudi fam miliyan 15 a duk kungiyar da take sha'awar sayen dan wasanta Daniel Sturridge, wadda kungiyar Sevilla ta nuna ra'ayinta akansa.
Dan wasan kungiyar Arsenal, Jack Wilshere, ya bayyana cewar zai bar kungiyar a yayin da kwantirakinsan ya kare a karshen watan yuni bayan ya shafe shekaru goma yana fafatawa a kungiyar ta Arsenal.
Your browser doesn’t support HTML5