Tun ranar 15 ga watan Yuni ne 'yan kungiyar Boko Haram suka afkawa garin Damboa inda suka yashe garin baki daya suka kuma hallaka mutane da dama lamarin da ya sa kawo yanzu babu wanda ya iya bada adadin wadanda aka kashe.
Yayin harin an kona masu duk gidajen dake garin da ma'aikatun dake ciki da kasuwanni da wuraren ibada. A makon jiya ne jami'an tsaron Najeriya suka fatattaki 'ya'yan kungiyar Boko Haram daga cikin garin Damboan bayan sun kwashe wata daya suna rike da garin.
Ganin irin barnar da 'yan Boko Haram suka yiwa garin ya sa dattawan garin suka mika kokon baransu ga gwamnatoci domin sake ginawa al'ummarsu matsuguni.
Shettima Afagu daya daga cikin dattawan yace kusan sati hudu kenan da 'yan Boko Haram suka kwace garin. Sun kashe wadanda suka iya kashewa . Sun kone gidaje wajen kashi 75 cikin 100. Sun hallaka dabbobi. Yanzu abun dake gabansu shi ne taimakon jama'arsu dake warwatse a sake tsugunar da su. Idan komi ya bi hanya kuma idan Allah Ya yadda mutanensu su fara dawowa. Amma kafin lokacin suna rokon gwamnatin jiha da ta tarayya su taimaka gidajen da aka kone a yi kokari a gyara saboda mutane su samu inda zasu sa kai kafin su fara shiga kasuwanci da noma.
Daruruwan al'ummar garin yanzu suna gudun hijira ne a wasu makwaftan jihohi ko kuma wasu garuruwan na daban.
Wakilin Muryar Amurka ya ziyarci wasu cikin masu gudun hijiran da suke zaune wurin da ake horon masu bautawa kasa. Wata Hajiya Kellu daga Damboa tace sun yi wata guda a wurin tare da yaranta. Ta nemi dakin haya amma kudin biyan hayan ne babu. A Damboan 'yan Boko Haram sun kashe mijinta sun barta da 'ya'ya tara da surukai.
Onarebul Haruna Daja Damboa na daya daga cikin mutanen dake garin Damboan da ya kawowa mutanen dake gudun hijira tallafi. Yace abun takaici ne a ce mutum dake da gidansa an gansa a cikin sassanin 'yan gudun hijira. Ya zama dole ta kowace hanya a taimaka masu. Shi Haruna yace 'yanuwansa mutane ashirin da daya babu wanda ya fito daga Damboa da komi illa suturar dake jikinsu.
A garin Gwoza kuma dake makwaftaka da Damboa mutane na cikin zaman dar dar domin har yanzu babu jami'an tsaro a garin kuma ba'a san inda sarkin garin yake ba.
Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.
Your browser doesn’t support HTML5