Kasar ba zata samu cigaba ba sai 'yan Najeriya sun hada karfi da karfe sun yaki son zuciya kafin a samu cigaba.
Kamar yadda Annabi Muhammed (S.A.W.) yace ba wani mummuni sai wanda yake so wa danuwansa abun da yake so wa kansa. Yace ya san mabiya addinin Kirista suma suna da kalma kamar haka wadda take neman hadin kai da taimakar juna. Sabili da haka Modibo yana kira, musamman arewacin Njaeriya tsakanin Musulmi da Kirista, tsakanin darika zuwa darika a bar wasu banbance banbance da kyamar juna da nuna kyashi da kiyayya tsakaninmu.
Idan an hadu an dinke babu wanda zai ga bayan al'ummar kasar. Amma muddin muka bari aka shigemu ana cewa kudu ta bangare ko arewa ta bangare to ba za'a samu zaman lafiya ba. Batun da a keyi yanzu ba na raba kasar ba ne. A'a yaya ma za'a yi kasar ta kara fadi ta habaka. Wata kasar ma ta shigo amma ba mu wargaje ba. Mutane su bar batun darika su duba manene Annabi ya koyar.
Ya cigaba da cewa addinin Musulunci ya nuna wa Musulmi yadda zai zauna da Musulmi danuwansa da Kirista da ma wanda bashi da addini. Kada ka taka hakinsa kada shi ma ya taka naka. Kada a dauka cewa domin mutum ba addininku daya ba ba garinku daya ba kuma kabilarku daya ba domin haka bashi da haki a kanka, yana da haki kuma wajibi ne ka bashi hakinsa. Tun da Allah ya hadamu a Najeriya to dole ne a zauna da juna cikin lumana. Mu jefa soyayya tsakaninmu. Makarantu ma su koyas da abubuwan da zasu hada kawunan mutane. Su koyas da kishin kasa. A guji raba kawunan jama'a.
Ga karin bayani.