Matsalar hare-hare ta fi muni a jihar Borno, jiha dake makwaftaka da kasashen waje uku.
An yi kyasin cewa fiye da kauyuka dubu daya da dari biyar ne 'yanbindiga suka debe daga jihar ta Borno yayin da manyan biranen jihar ke fama da kwararowar jama'a daga kauyukan da 'yan Boko Haram suka mamaye.
Harin baya-bayan nan shi ne na garin Gwoza inda 'yanbindigan suka kwace shugabancin garin suka kashe na kashewa suka fatattaki sauran mutanen garin. Haka kuma sun kwashe kayan abinci da dukiyoyi da motocin dake garin. Duk wani matashi kuma da suka gani a garin sun bindigeshi har lahira kamar yadda wani da ya samu kubuta ya tabbatar.
Duk lokacin da mutum ya ziyarci wuraren da 'yanbindigan suka kai hari babu abun gani sai gine-gine da ababen hawa da aka kone. Abun ban tausayi sai kananan yara da suke kukan fitan hankali sakamakon halin da suka samu kansu musamman wadanda aka kashe iyayensu.
A wata makarantar firamare fiye da mutane dubu biyar suka fake wurin domin neman tsira da rayukansu.
A halin da ake ciki wasu mafarauta suna neman izini daga gwamnatin tarayya domin zuwa nemo 'yan matan nan na Chibok da aka sace a watan Afrilu. Abdulkarim Baba Mai Giwa ya shaidawa wakilin Muryar Amurka cewa sun tara mafarauta fiye da dubu biyu amma gwamnatin tarayya bata basu izini ba.
Sanata Muhammed Ali Ndume dan majalisar dattawa mai wakiltar kudancin Borno da ta hada da Damboa da Gwoza ke karkashinsa yace sun hadu su roki jami'an tsaro su hanzarta su kwato wuraren da 'yan Boko Haram suka mamaye kwana kwanan nan.
Ga cikakken rahoto na musamman da Haruna Dauda Biu ya shirya.