Dattawan Arewa Sun Yi Watsi Da Matsayar Gwamnonin Kudu Na Baiwa Yankin Kudu Shugabanci A 2023

  • Murtala Sanyinna

Kungiyar Dattawan Arewa.

Kungiyar ta ce ba wani yanki da za’a ce tilas shi ne zai samar da shugabancin kasa a tsarin dimokaradiyya, domin kuwa mukami ne da ake zaben kowane mutum, kuma daga ko wane yanki ya fito.

Kungiyar Dattawan Arewa ta yi watsi da matsayar da gwamnonin yankin kudu suka cimma, na cewa wajibi ne shugaban kasa ya fito daga yankin kudu a zaben shekara ta 2023.

A cewar kungiyar, kujerar shugaban kasa mukami ne da ake samu ta hanyar dimokaradiyya, ba wai tsarin karba-karba ba.

Kungiyar tana mai da martani ne akan matsayar da gwamnonin kudancin Najeriya suka cimma a wani taro da suka yi a birnin Ikko a ranar Litinin, inda suka ce tilas a baiwa yankin na kudu damar fitar da shugaban kasa, bayan karewar wa’adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

“Kungiyar ta amince a mataki na bai daya cewa, a rika mulkin karba-karba tsakanin kudanci da arewacin Najeriya. Ta kuma amince cewa, shugaban Najeriya na gaba, ya fito daga yankin kudanci.” In ji sanarwar da kungiyar ta fitar a karshen taron na Legas, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Odunayo Akeredolu.

Kazalika gwamnonin sun kara jaddada matsayarsu ta cewa Najeriya ta ci gaba da zama a matsayin kasa dunkulalliya bisa tsari na adalci.

Gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya a wani taro da suka yi a watan Nuwamban 2020 (Facebook/David) Umahi

To sai dai kuma a sanarwar mai da martani da kungiyar ta dattawan Arewa ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta Dr. Hakeem Baba Ahmed, ta ce Arewa ba za ta bari ayi mata baranaza akan ta bar hakkinta na dimokaradiyya ba.

Kungiyar ta ce ba wani yanki da za’a ce tilas shi ne zai samar da shugabancin kasa a tsarin dimokaradiyya, domin kuwa mukami ne da ake zaben kowane mutum, kuma daga ko wane yanki ya fito.

Haka kuma kungiyar ta bayyana matsayar gwamnonin na Kudu a matsayin “nuna son kai” wanda ta ce lamari ne da ya kamata a warware ta hanyar tsarin siyasa da dimokaradiyya.

“Muna a cikin gwamnatin dimokaradiyya ne, kuma cimma matsayar yankin da zai shugabanci kasa abu ne da za’a yi ta hanyar tsarin dimokaradiyya da baiwa ‘yan kasa hakkinsu na zaben shugaban da suke so” in ji sanarwar.

To sai dai kungiyar ta dattawan Arewa ta shawarci gwamnonin na kudu da cewa kamata yayi su gamsar da jam’iyyun siyasarsu da su tsayar da dan takarar shugaban kasa daga jihohin kudu, kana kuma su yi aiki tukuru wajen gamsar da ‘yan Najeriya daga dukkan sassan kasa da su zabi dan takarar na su.

Kungiyar Dattawan Arewa

Kungiyar ta kara da cewa “ba zai yiwu a kwacewa ‘yan Najeriya ‘yancinsu na zaben shugaban da suke muradi ba ta hanyar wata barazana da cin zarafi,” ta ci gaba da cewa “’yan siyasa a yanzu sun zama raggaye da suke tunanin kawai a ba su shugabanci ta hanyar wa’adi da karba-karba” a maimakon yin aiki tukuru wajen samun mukaman siyasa.

Wannan lamari dai na ci gaba da haifar da cece-kuce, musamman tsakanin yankunan kasar biyu, a yayin da matsayar gwamnonin ta ke ci gaba da fuskantar turjiya da rashin amincewa musamman daga yankin Arewa.