Daruruwan 'Yan Kungiyar Asiri Sun Shiga Hannu a Najeriya

Babban sifeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim K. Idris

Rudunar 'yan sandan jihar Oyo da majalisar jihar na daukar matakan kare jihar daga 'yan kungiyoyi asiri da suka zama ruwan dare a yankin.

A kokarin da ta ke yi na kare jihar Oyo, daga muggan ayyukan ‘yan kungiyar asiri da suka addabi makwabtan jihohin Lagos da Ogun, rudunar ‘yan Sandan jihar Oyo, ta kama daruruwan ‘yan kungiyoyin asiri domin hanasu afkawa jama’ar jihar.

Kwamishinan ‘yan Sanda na jihar Abiodun Odude, ne ya shedawa taron ‘yan jarida hakan a lokacin da yake yi masu jawabi a garin Ibadan.

Ya kara da cewa rundunar tana kokari wajen magance matsalolin kungiyar asirin nan da suka addabi jama’a da ake kira “One Million Boys” da “Idomie Boys” a cikin watanni hudu da suka gabata sun gabatar da fiye da mutane 500.

Ya ce wasu masu aikata laifuffuka dake fakewa da kungiyoyin asiri suna razana mutane da adduna da wasu muggan makamai.

Su kuwa kungiyar Badoo Boys ba wata kungiya ce ta masammam ba face itama kungiya ce ta asiri kamar sauran kungiyoyin asiri amma su suna yankin Ikorodu ne a jihar Lagos, inda suke cin karensu babu babbaka in ji kwamishinan ‘yan Sandan.

Shugaban majalisar dokokin jihar Oyo, Michael Adeyemo, ya ce majalisar jihar tana cikin shirin ko-ta-kwana domin tunkarar duk abinda ka iya tasowa na kungiyar asiri domin tabbatar da kariya ga al'umar jihar ta Oyo.

Your browser doesn’t support HTML5

Daruruwan 'Yan Kungiyar Asiri Sun Shiga Hannu a Najeriya-2'29"