Daruruwan Masu Zanga Zanga Sunyi Maci Zuwa Fadar Shugaban Kasa

Jiya Litini daruruwan 'yan Najeriya masu zanga-zanga sun yi maci zuwa Fadar Shugaban Kasa a Abuja, babban birnin kasar, inda su ka bukaci gwamnati ta kara azama kan batun ceto 'yan mata sama da 200 din nan da aka sace a 2014.

Zanga-zangar ta zo ne sati guda bayan da mayakan nan masu tsattsauran ra'ayi na Boko Haram su ka fitar da wani faifan bidiyo mai nuna 50 daga cikin 'yan matan da aka sacen. Kungiyar mayakan ta ce da dama daga cikin 'yan matan sun mutu, kuma ta na na bukatar a yi musayar fursunoni da sauran da su ka rage.

Esther Yakubu, mahaifiyar daya daga cikin 'yan matan da aka sace, masu zanga-zangar sun ma gaji da rawan rubuta takardar koke ga gwamnati na nemar a ceto 'yan matan.

Daya daga cikin 'yan matan da aka nuna a bidiyon diyar Esther Yakubu ce.

Ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta biya bukatar 'yan Boko Haram saboda a saki diyarta Dorcas da sauran wadanda aka sacen.