Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tsagerun Niger Delta Avengers Ta Dakatar Da Kai Hare Harenta


Avengers
Avengers

Kungiyar ‘yan bindigar Niger Delta ta Avengers ta ce zata mutunta kiraye kirayen da ake mata na dakatar da kai hare hare kan duk wasu kamfanonin hakkar Mai a yankin.

A baya bayan nan ne wasu dattawan yankin Niger Delta, suka bukaci ‘yan bidigar su kawo karshen hare haren da suke kaiwa don a sami damar tattaunawa da gwamnatin tarayyar Najeriya, saboda a karawa yankin kudaden da ake samu daga Mai a yankin.

Sai dai kuma duk da cewa ‘yan bindigar na Avengers sun dakatar da kai hare hare a yankin na Niger Delta, har yanzu dai ana ci gaba da kai hare hare kan kamfanonin ayyukan hakar Mai. Hari na baya bayan nan dai shine wanda wata kungiya dake da suna Justice Mandate, ta yi ikirarin kaiwa tare da fasa wasu bututun Mai a yankin.

A wani al’amari mai karo da wancan shine wata sabuwar kungiya a yankin na Niger Delta, tace zata ci gaba da gwagwarmayar da take da dinbin makamai a yankin.

Saurari cikakken rahotan Lamido Abubakar Sokoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:14 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG