Dangote Ya Ce Za A Kammala Ginin Matatar Mai Na Najeriya A Kwata Na Hudu

Aliko Dangote

Kamfanin matatar mai na Dangote mai iya samar da 650,000(bpd)  na mai a kowace rana, wanda ake ginawa a Najeriya, zai fara aiki nan da kwata na hudu na shekarar 2022, in ji Babban Darakta rukunin kamfanin, Devakumar Edwin a ranar Lahadi.

“An kamala kashi 75% na duk wasu gwaje-gwajen na’urorin da ke amfani da wutar lantarki gabanin shirye-shiryen kammala aikin matatar a cikin kwata na hudu na wannan shekara,” abin da Edwin ya ce kenan yayin rangadin wuraren da Ministan Yada Labarai na Najeriya, Lai Mohammed ya yi.

Matatar man da ake ginawa kan kudi dala biliyan 19 a Legas, tana da karfin ajiyar lita biliyan 4.74 inji Edwin. Ya kara da cewa kashi 75% na kayayyakin za a rika jigilar su ne ta jirgin ruwa a cikin Najeriya.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya ce a watan Janairu yana sa ran aikin matatar mai zai fara aiki a karshen kwata na uku.

An jinkirta aikin da shekaru da dama kuma kudin ya kai dala biliyan 19 daga kiyasin da Dangote ya yi a baya na dala biliyan 12 zuwa dala biliyan 14.

Ku Duba Wannan Ma Buhari Ya Kaddamar Da Kamfanin Taki Na Dangote A Legas

Dangote, wanda ya gina arzikinsa a masana’antar siminti, ya fara bayyana aniyar gina matatar mai a shekarar 2013, inda a lokacin aka sa ran kammala aikin a shekarar 2016.

Daga nan ne attajirin ya koma Lekki da ke Legas, inda ya inganta girman masana’antar kuma ya ce za a fara samar da shi a farkon shekarar 2020.

Duk da cewar Najeriya babbar kasa mai samarwa da kuma fitar da man fetur a Afirka ce, ta dogara kusan kacokan kan shigo da mai bayan ta yi sake da ya yi sanadin dusashewar man da ta ke samarwa cikin shekaru da dama.

A watan da ya gabata Dangote ya kaddamar da wani kamfanin takin zamani na dalar Amurka biliyan 2.5, wanda tuni yake fitar da su zuwa kasashen Amurka, Indiya, Brazil, Mexico da Argentina.

~ REUTERS