Dangote Na Sa Ran Buhari Zai Kaddamar Da Kamfanin Matatar Mansa Kafin Wa’adinsa Ya Kare

Aliko Dangote

Wani Ma’aikacin kamfanin Dangote ya ce a wannan watan matatar man za ta fara aiki a kwata na hudu na shekarar 2022.

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya ce a ranar Juma’a ana sa ran fara aikin matatar mai da ya kai ganga 650,000 a kowace rana a shekara mai zuwa, kafin wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare.

Ana gina matatar man ne kan kudi dala biliyan $19 a Legas wanda aka yi ta jinkirta shi shekaru da dama, lamarin da ya kara kudin da Dangote ya kiyasta a baya na dala biliyan $12- $14 kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

"Da yardar Allah, shugaban kasa zai zo ya kaddamar da matatar man kafin karshen wa'adinsa a shekara mai zuwa," in ji Dangote yayin da yake amsa tambayar bayan ganawarsa da Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Wani Ma’iakatan kamfanin Dangote ya ce a wannan watan matatar man za ta fara aiki a kwata na hudu na shekarar 2022.

Gwamnati na kallon matatar a matsayin mafita ta kawo karshen dogaron da Najeriya ke yi na shigo da man fetur mafi yawa duk kuwa da cewa Najeriya ce kan gaba wajen samar da man fetur da fitar da man a Afirka.

Jami’an gwamnati sun ce sun fara inganta wasu matatun mai na wasu jihohi wadanda ke da karfin tace ganga 445,000 a kowace rana (bpd) amma sun lalace cikin shekaru da dama da suka wuce.

~ REUTERS