Dangin Namitra Bwala, dalibar kwalejin “Lead British International School” dake Gwarinpa, a birnin Abuja, sun maka makarantar a kotu.
Shigar da karar ya biyo bayan faifan bidiyon daya karade shafukan sada zumunta a ‘yan makonnin da suka gabata inda aka ga wasu dalibai suna cin zalin Namitra Bwala.
Haka kuma dangin dalibar na neman diyar Naira milyan 500, da neman gafara a jaridun Najeriya guda 2 saboda gazawar makarantar wajen sauke nauyin daya rataya a wuyanta na samawa ‘yarsu kyakkyawan yanayin neman ilimi.
Karar wacce aka shigar gaban Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja, tace gazawar makarantar wajen hana cin zalin dalibar, tare da gaggauta sanarda iyayenta da kuma gudanar da bincike akan lamarin har sai da bidiyon afkuwarsa ya karade shafukan sada zumunta alhalin tana karkashin kulawar makarantar, ya tabbatar da cewar akwai sakaci.
Sun kuma bayyana fatan cewar karar zata samar da gagarumin sauyi tare da daukar matakan da suka dace wajen hana afkuwar makamancin hakan a makarantar a nan gaba.