Tankiya tsakanin Amurka da China ta ‘kara tsanani a jiya Asabar, yayin da ma’aikatar harkokin wajen China ta kira jakadan Amurka a China Terry Branstad, domin rashin jin dadinta kan takunkumin da Amurka ta sakawa China, saboda ta sayi wasu jiragen yaki da makamai masu linzami da ga Rasha.
Wannan dai na faruwa ne ‘yan sa’o’i bayan da China ta soke zaman tattaunawa kan cinikayya da Amurka, saboda matsayar Amurkar na ‘kara sabon haraji akan kayayyakin China.
Wata sanarwa da aka kafe da shafin yanar gizon ma’aikatar harkokin wajen China na cewa “hakan yayi matukar sabawa dokar kasa da kasa.” Da kuma ji da kai. Haka kuma ma’aikatar ta rubuta cewa “Harkokin China da Rasha harka ce ta kasashe biyu masu diyauci, kuma Amurka bata da wani hurumin yin katsalandan. Kuma matakin da Amurka ta dauka ya lalata dangantarta da China.
Tun farko dai China ta nemi Amurka da ta janye takunkumin da ta saka, kuma da yake magana da manema labarai mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Geng Shuang, ya ce China ta rubuta takardar nuna bacin ranta a hukumance ma Amurka.
Sayen makaman da China ta yi daga Rasha ya keta dokar Amurka da aka saka a shekarar 2017, domin hukunta shugaban Rasha Vladimir Putin kan katsalandan din da Rashar ta yi a zaben shugaban Amurka, da sauran wasu harkoki.