Danbaba Suntai Yana Samun Sauki In Ji Mukaddashin Gwamna Garba Umar

Gwamna Danbaba Suntai na Jihar Taraba, yana tattaunawa da ma'aikatan VOA Hausa kafin btaron yaki da cututtuka a Jalingo a watan Yunin 2010.

Mukaddashin gwamnan, wanda ya duba Suntai a asibiti a Amurka, yace jikin gwamnan yayi sauki sosai in an kwatanta da yadda yake kwanakin baya a kasar Jamus
Mukaddashin gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Garba Umar, yace jikin gwamna Danbaba Suntai yayi sauki sosai idan an kwatanta da yadda yake kafin a dauke shi daga Jamus a maido da shi zuwa wani asibiti a nan kasar Amurka.

Mukaddashin gwamnan, wanda ya ziyarci gwamnan a inda ake masa jinya a Amurka, yace Mr. Suntai yana samun sauki, kuma sun gaisa sosai har ma ya gode masa a kan yadda yake rike ragamar harkokin jihar Taraba.

Alhaji Garba Umar ya ce, "...daga gani na (Suntai) ya tashi, muka kama hannun juna yana ce mini ya gode, ya gode. Yayi murmushi, aka kuma dauke mu a hoto, wanda aka nuna a duniya kowa ya gani."

Mukaddashin gwamnan yace a bayan nan babu wata maganar da suka yi.

A kan ko yaushe gwamna Danbaba Suntai zai komo Jalingo, mukaddashin gwamnan yace ,likitocin da suke duba shi ne zasu yanke wannan shawara.

Akwai jita-jita da yawa cewar ana wani yunkurin dauko gwamnan a maida shi Najeriya, duk da cewa bai kammala warkewa ba.

Ga cikakken rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko daga Abuja, kan tattaunawar da shi mukaddashin gwamna Alhaji Garba Umar, yayi da 'yan jarida, da kuma iri n martanin da masu sharhi suka mayar kan batun.

Your browser doesn’t support HTML5

Mukaddashin Gwamna Garba Umar Na Jihar Taraba Yace Danbaba Suntai Yana Samun Sauki - 2:25