Chief Anyaoku ya yi wannan hurucin ne a birnin Ibadan babban birnin jihar Oyon Nageriya. A jawabin nasa ya bukaci duk 'yan siyasar Najeriya da su hada hannu da gwamnatin kasar domin a shawo kan kowace irin matsala musamman rashin tsaro da ya zama ruwan dare gama gari.
Chief Anyaoku ya kara da cewa yin anfani da siyasa zai shawo kan duk wata kalubale na kungiyar Boko Haram. Ya ce yin anfani da amintattun mutane daga shiyoyi shida na kasar zai samo bakin zaran duk wata matsala da zai anfani kasar gaba daya ya kuma taimaka kasar ta zama tsintsiya madaurinki daya. Ya ce a kasashe kamar su Ingila da Amurka yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban na hada kai idan aka samu rigingimun 'yan ta'ada. Don haka ya kamata 'yan siyasar Najeriya su yi koyi da su.
Shi ko gwamnan jihar Oyo a nashi jawabin cewa ya yi yin taron sulhu na kasa zai bada zarafin sake duba kundin tsarin mulkin kasar. Yin hakan zai zama da alfanu a harkokin gwamnati da mulki. Ya ce gwamnatin Oyo zata hada kai da duk abun da zai ingata zaman lafiya a Najeriya da kuma hada kan kasar gaba daya.
Hassan Umar Tambuwal nada rahoto.