Dan Wasan Tottenham Dele Alli Ya Sabunta Kwantiraginsa

Dan wasan tsakiya na Tottenham dan kasar Ingila Dele Alli ya sanya hannu a sabon kwantiragi inda da zai ci gaba da zama a Kungiyar har zuwa shekarar 2024.

Dan wasan mai shekaru 22 da haihuwa ya koma Tottenham ne akan kudi fam miliyan £5m a shekara ta 2015, bayan komawarsa ya samu nasarar zura kwallaye 48 a raga cikin wasa 153 da ya buga wa kungiyar ta Tottenham.

Ku Duba Wannan Ma Sau Nawa Barcelona Da Real Madrid Suka Kara?

A bana dan wasan ya buga wasanni shida a gasar Firimiya ciki kuwa har da inda suka kaye a hannun Manchester City ranar Litinin a filin wasa na Wembley - da ci 1-0.

Ko da yake, har yanzu dan wasan bai zura kwallo ba tun da aka soma gasar sai dai a wasan Dele ya shigo ne a matakin canji lokacin an sha su 1-0.

Dele ya koma kulob din ne daga tsohowar kungiyar matasa ta MK Dons inda ya fara taka leda tun yana dan shekaru 16 a duniya.

Alli ya bi sahun takwarorinsa na kulob din irin su Harry Kane da Son Heung-min da kuma Harry Winks wajen sanya hannu a sabon yarjeniyar tsawaita kwantaragin da kungiyar ta Tottenham.

Your browser doesn’t support HTML5

Dan Wasan Tottenham Dele Alli Ya Sabunta Kwantiraginsa 2'20