Rahotanni na nuni da cewar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, za ta yi asarar zunzurutun kudin da ya kai Euro miliyan 18, kwatankwacin fan miliyan (£16m) kudin Ingila in har ta sallami kociyanta Julen Lopetegui, Mai shekaru 52, da haihuwa.
Kungiyar dai tana duba yiwuwar sallaman kocin ne bayan irin koma bayan da take samu a wasanni inda aka kididdigar cewar ta buga wasanni na tsawon mintuna 482 ba tare da ta sanya kwallo a cikin raga ba wadda hakan wani mummunan tarihi ne a gareta.
Lopetegui wanda tsohon kocin tawagar yan wasan kasar Spain ne da ta sallame shi yayin da ake shirin buga gasar cin kofin duniya 2018 a Rasha, bayan da ta samu labarin ya karbi aiki da kulob din Real Madrid, sakamakon kocin Zinedine Zidane, ya ajiye aikinsa a kungiyar ta Real a rana tsaka.
Real dai ta dauki kocin ne a yarjejeniyar kwantiragin shekaru uku zuwa 2021.
Sai dai kafin cikar wa'adin da yiwuwar sallamar shi a aikin domin rashin samun abin da ta ke bukata daga gare shi, inda yanzu take matsayi na bakwai a teburin La Liga a yayin da aka shiga mako na tara a bana.
Sai dai kuma a ranar talata kungiyar ta samu nasara akan Viktoria Plzen da ci 2-1 a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a matakin wasan rukuni zagaye na uku daga rukunin (G) hakan ya sanya take matsayi na biyu a rukunin da maki shida, Roma tana samanta ita ma da maki shida inda kwallo ya banbanta su.
Wasu bayanan na nuni da cewar in har ta sallame shi akwai yiwuwar tsohon kocin Chelsea Antonio Conte ya maye gurbinsa kuma za ta biya Lopetegui kimanin fan miliyan 16 sakamakon sallamar da ta masa yana da sauran shekaru a yarjejeniyar da suka yi da kulob din kamar yadda doka ta tanadar.
Facebook Forum