Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA: Sabon Matsayin Najeriya a Fagen Kwallon Nahiyar Afirka


Shugaba Buhari Tare Da Kungiyar Kwallon Kafa Na Kasa Super Eagles
Shugaba Buhari Tare Da Kungiyar Kwallon Kafa Na Kasa Super Eagles

Tawagar kungiyar kwallon kafar Super Eagles a Najeriya ta yi abin bajinta inda ta matsa gaba da mataki 4 a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke fitarwa a duk karshen wata kan kasashen da suka fi iya kwallo, inda yanzu ta haura mataki 44 a Duniya.

Jadawalin da hukumar ta wallafa a shafinta na ranar Alhamis ya nuna cewa yanzu Najeriya na da maki 1,431 a wannan watan fiye da na watan Satumba Inda ta ke da maki 1,415.

Jadawalin na hukumar FIFA dai ya nuna cewa yanzu Najeriya ita ce kasa ta uku mafi iya kwallo a Nahiyar Afrika, bayan kasashen Tunusia da Senegal da suke samanta.

Ana dai ganin wannan nasara da Super Eagles ta samu cikin sauri na da nasaba da irin nasararta kan kasar Libya da ci 4-0 a gida da kuma ci 3 da 2
a waje, yayin wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Afrika wanda za'ayi a badi a Kamaru.

Ita Tunisa ita ke matsayin ta 22 a Duniya sai Senegal a matsayin ta 24, yayin da kasashen Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo, da Morocco ke matsayin na 46 da 47 cikin kasashe 50 mafiya iya kwallo a Afrika.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG