Dan Wasan Liverpool Flanagan Zai Je Gidan Kangararru

An tura dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool John Flanagan, gidan gyaran halayyar kangararru, tare da aikin awa 40, batare da biyan shi ko kwandala ba, an yanke masa wannan hukunci ne a sakamakon amincewar da yayi na kaima budurwarshi hari.

Dan wasan mai shekaru 25, da haihuwa ya amince da laifin lakadama budurwar shi duka. A ranar 2 ga watan Jamairun nan, wata Kotu a birnin Liverpool ta saurari karar cewar ya yi fatali da kayan abokiyar zaman shi daga gidansa ya barta tana walagigi a babban titin dake tsakiyar birnin Ingila, da ke arewa maso yammacin birnin, da sanyin safiyar ranar 22 ga watan Disambar bara.

Mai shari'a a kotun karamar hukumar Wendy Lloyd, ta yanke mashi hukuncin watanni 12 na ayyukan taimako a yankin, wanda ya hada da ayyukan gyara hallayen kangararru na kwanaki 15, da kuma tarar kotu ta dallar Amurka $117.

Mai shari'ar ta kara da cewar, duk da kasancewar sa matashi ne mai halayen kirki, amma abun takaici ne da ya samu kansa a cikin wannan yanayi, lauyansa Mr. Lionel Grieg, ya bayyana cewa kotun ta yanke wannan hukunci ne biyo bayan kallon bidiyon da ya bayyana yadda ta kasance tsakanin matashin da budurwar sa.