Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Yada Wasan Cikin Kofin Duniya Kai Tsaye Ta Twitter, Snapchat, Fox's


Gidan talabijin na Fox’s Sport, tare da hadin gwiwar kamfanonin Twitter, da Snapchat, sun kammala duk shirye shiryen da suka kamata don daukar nauyin wasan gasar cin kofin duniya, kai tsaye da za’a gabatar a karshen shekara.

Gidan talabijin na Fox, zai shirya wasan, inda su kuma kafofin yanar gizo zasu yada shi a duniya baki daya, wasan da za’a gabatar a kasar Rasha, wanda za’a rika nuna wasannin da aka gabatar a baya da abubuwan da za’ayi kafin wasan.

Gidan talabijin na Fox ya tabbatar da cewar za’a yada wasan a baki dayan kasar Amurka, idan mutane nada bukatar kallo kai tsaye sai su shiga shafin twitter @FOXSport, da FOXSoccer.

Haka kuma gidan talabijin din zai gabatar da mujallar wasannin wanda za’a wallafa a shafufukan twitter da snapchat, inda za’a rika nuna duk abubuwan da suke gudana a kowace rana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG