Dan Wasan Chelsea Didier Drogba Na Shirin Ritaya Daga Murza Leda

Tsohon dan wasan gaba na Kungiyar Kwallon kafa ta Chelsea Didier Drogba ya bayyana ajiye takalman wasansa bayan da ya shafe shekaru 20 ya na murza tamola.

Dan wasan dan kasar Ivory Coast mai shekaru 40, da haihuwa a lokacin da yake Kungiyar Chelsea, ya zurara kwallaye 164 a raga cikin wasanni 381 da ya buga, haka kuma ya samu nasarar daukan kofin firimiya lig na kasar Ingila sau hudu da lashe gasar zakarun turai Uefa Champion League na shekara 2012, da kofin kalu bale (FA) sau hudu duk tare da tawagar Chelsea.

Haka zalika, ya kasance gwarzon danwasan da yafi zurara kwallaye (Golden Boot) a gasar firimiya lig na shekarun 2006-2007 da kuma 2009-2010.

Ku Duba Wannan Ma Manyan Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Duniya Sun Shiga Riga Daya

Bayan ya bar Kungiyar ta Chelsea Drogba, ya koma kulob din Shanghai
Shenhua, dake kasar Sin inda ya buga mata wasa na tsawon watanni shida kacal, daga bisani ya koma Galatasaray, na tsawon shekara daya da rabi kafin ya sake dawowa tsohowar kulob din sa Chelsea.

A wasannin da ya buga wa kasar sa Ivory Coast, kuwa ya fafata wasanni har guda 105 ya jefa kwallaye 65 ciki hadda wasanni cin kofin duniya sau uku.

Ya kuma lashe kyautar gwarzon danwasan kwallon kafa na Afirka sau biyu, daga karshe ya kammala watanni 18 na wasannin sa tare da tawagar Phoenix Risin dake Amurka.

Drogba yace lokaci yayi da ya kamata yayi ritaya daga buga wasa bayan ya shafe shekaru ashirin a fagen daga.