Tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Ingila, wanda yafi zurara kwallaye a tarihi kulob din Wayne Rooney, zai kasance kaftin din tawagar kasar a wasan da za su yi da Amurka a yau Alhamis.
A wani wasa na sada zumunci domin karrama dan wasan, hakan na nuni da cewar Rooney yayi bankwana da tawagar Kungiyar kwallon kafa ta Ingila kenan.
Sai dai tuni dama dan wasan mai shekaru 33 da haihuwa, ya yi ritaya daga bugawa Ingila wasanni tun a shekarar 2017, amma duk da haka zai buga wasansa na karshe, kuma wannan wasan shine ciko na 120 da zai yi a yau.
Sai dai dan wasan Ingila Fabian Delp shi zai fara daura kambun Kaftin din tawagar ta kasar Ingila, kafin daga bisani ya mika kambun ga Wayne Rooney, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Ka zalika za'a karrama Rooney na musamman a yau don tuna irin gudunmawar da ya bayar a bangaren kwallon kafa wa kasar ta Ingila yayin da yake kan ganiyarsa.
Wayne Ronney ya samu nasarra zurara kwallaye har guda 53 a wasannin da ya buga wa Ingila, kafin ajiye takalman wasan.
Yanzu haka dai dan wasan Rooney ya na taka ledarsane a Kungiyar kwallon kafa ta DC United dake kasar Amurka bayan da yabar Manchester United.
Za'a buga wasanne da misalin karfe tara na yammaci agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Chadi.
Facebook Forum