Kwalejin, wadda sanatan Kano ta tsakiya a majailisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau ya gina, a wani bangare na ayyukan raya mazabu da ‘yan majalisar dokoki a Najeriya ke yi, nada girman azuzuwa da zasu dauki yawan dalibai dari biyar a lokaci guda.
Kazalika kwalejin, wadda za ta kunshi maza da mata dalibai, nada dakunan kwana da filin motsa jiki da kuma gidajen malamai.
Bayan bude kwalejin, dan takarar na PDP ya wuce zuwa fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, inda ya nemi tabarriki da kuma samun goyon bayan masarautar Kano domin samun nasara a zabe, yana mai nanata kudirorinsa na hada kan ‘yan kasa da tabbatar da tsaro da kuma farfado da tattalin arziki.
A jawabinsa, mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi fatan alkahiri ga dan takarar tare da tunasar da shi bukatar dake akwai ta kyautata wa al’umma muddin aka sami nasara a zabe.
Bayan barin sa fadar Kano, Alhaji Atiku Abubakar ya wuce zuwa filin wasan kwallon kafa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano, inda zai gabatar da jawabi ga dinbin magoya baya.