Tun daga kidayar kuri'ar zaben fidda gwani na babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP don babban zaben da ke tafe a ka fahimci Atiku Abubakar ne zai lashe kamar yanda ya lashe irin wannan zaben a 2019.
Atiku wanda a wani lokacin a ke ganin ya kan kafa jam'iyyar ko-ta kwana don kar ya rasa wajen tsayawa tun sabanin su da tsohon shugaba Obasanjo a 2007 ya yi bayani kan jam'iyyar PDM.
An yi ta yayata cewa, Atiku ya kafa PDM ne don in ya rasa takara a PDP sai ya sauya sheka zuwa PDM ya yi takarar, “tun zamanin Babangida PDM na nan bai yi ma ta rejista ba, Abacha ma bai yi ma ta rijista ba, daga sunanta ne ma a ka samu PDP don haka mu na aiki tare wasu sun shiga PDP wasu kuma ANPP”
An haifi Atiku a 1946 a yankin Jada na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya kuma nemi takarar shugabancin Najeriya sau biyar kenan in an hada da zaben nan na 2023 inda ya ci nasarar samun tikiti sau uku.
Atiku, wanda tsohon jami'in kwastam ne, ya fara neman tikitin takara a 1993 inda Moshood Abiola ya samu tikitin na SDP.
A 2007 ya na matsayin mataimakin shugaban Najeriya ya nemi takara a jam'iyyar AC da su Tinubu su ka yi amfani da ita wajen shiga APC.
A 2011 ma Atiku ya gwada nema a PDP inda shugaba a lokacin Goodluck Jonathan ya samu tikitin.
Atiku ya sake nema a APC a 2015 amma shugaba Buhari ya samu tikitin. A 2019 Atiku ya yi takara a PDP ya zo na biyu a yawan kuri'u in an gwada da shugaba Buhari na APC.
Yanzu ga Atiku a PDP don zaben nan na 25 ga Fabrairu.
Jigo a PDP Attahiru Bafarawa, ya ce ko kusa ba za a kwatanta gogewar Atiku da sauran 'yan takara ba, ya na mai buga misali da Bola Tinubu na APC
“A arewa ba za a kwatanta Bola Tinubu da Waziri ba, a kudu ba za a gwada ba, duk mai kishin Najeriya sai ya zabi Atiku Allah ya taimake shi ya kawo ma na sauyi.”
Baya ga zargin bakin jini da PDP ta yi a baya har masu hamayya da Atiku ke alakanta shi da almundahana duk da ba cajin da a ka taba yi ma sa, 'yan APC sun kalubalance shi ya shiga Amurka in ya isa kuma Atiku ya shiga Amurka lamarin da ya kwantar da batun.
Da zarar dawowar shi gabanin zaben 2019, Atiku ya amsa gayyatar wata muhawarar takarar shugaban kasa inda bangaren shugaba Buhari ba su halarta ba.
Atiku ya fice daga taron ya na mai cewa dama shugaba Buhari ne ya ke son su yi muhawara don shi ya ke kan mulki amma sauran ‘yan takara da su ka zo babu amfanin muhawara da su.
Dan tawagar kamfen din PDP Abdul Ningi, ya ce Atiku ne kadai ke da zimmar tunkarar APC a zaben.
Ningi ya wanke Atiku da nuna cewa ba ya nuna bambanci don addini, kabila ko yanki “ba ya fassara ka don babbar rigar ka.”
Yanzu dai sai a jira a ga yanda zaben na 25 ga watan Fabrairu nan zai kaya da a ke ganin shata dagar, ta fi karfi tsakanin PDP, APC, NNPP da Leba; wato tsakanin manyan ‘yan takara Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Rabi’u Musa Kawnkwaso da Peter Obi.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya cikin sauti: