Wani dan takarar kujerar Majalisar dattawan Najeriya daga yankin gabashin jihar Naija, karkashin jam’iyyar adawa ta ADP, Muhammad Bashir Abacha, ya maka hukumar zaben mai zaman kanta ta INEC da kuma Jam’iyyar ADPa gaban wata kotun tarayya da ke Minna.
Ya dai shigar da karar ce a gaban kotu saboda rashin sanya hoton jam’iyyar ADP a jikin takardar kada kuri’a lokacin zaben 'yan majalisa dokokin Najeriya da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Muhammad Bashar Abacha ya ce, ya je kotu ne a matsayinsa na dan kasa wanda aka "cuta" don a kwato ma su hakkinsu da kuma hakkin jama’arsu da suka ringa shiga "lungu da sako ba dare ba rana" don neman kuri’un mutane.
Sannan ya kuma kara da cewa sun fito ranar zabe amma wasu daga sama sun "cucesu" sun siyar ma su da ‘yancinsu, saboda haka suka zo wannan kotu kuma suna tunanin za a yi ma su adalci.
Shi ma lauyansa, Barista Abubakar Indaku Musa, ya ce, jam’iyyarsa, sun ba shi takarar Sanata, amma wasu sun yi amfani da mukaminsu sun hana shi wannan takara wanda ‘yancin dokar kasa ta ba shi.
Sai dai hukumar zabe ta INEC reshen jihar Naija ta hannun mai magana da yawunta Ibrahim Abari, ya ce hukumar ba ta lura da cewa babu tambarin jam’iyyar ADP a takardar kada kuri’ar ba, amma ta ce za ta duba wannan lamarin.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna:
Your browser doesn’t support HTML5