Yayin da ake haramar zaben gwamnoni a ranar Asabar mai zuwa a Najeriya, yanzu haka anja daga a tsakanin jam’iyyar APC da ke mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Adamawa, mahaifar dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa Atiku Abubakar.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ce ta lashe zabe a jihar Adamawa a babban zaben shugaban kasa da ya gabata inda ta samu kujerun majalisar wakilai da na dattawa biyu, lamarin da ya kai jam’iyar APC soma daura damara domin tunkarar zaben gwamna da ke tafe.
Tuni jam’iyyar ta APC kira wani taron sirri na ganin ba ta rasa kujerar gwamnanta ba a zaben da ke tafe.
Dr. Umar Duhu,tsohon shugaban riko ne na jam’iyar ta APC a shiyar arewa maso gabas,ya ce sun dau darasi a yanzu.
Da farko dai an danganta faduwar jam’iyyar ta APC a Adamawa da rikicin cikin gida da take fama da shi.
Mr. Boss Gida Mustapha sakataren gwamnatin tarayya, ya ce a wannan karon APC za ta kare kujerarta.
Kamar 'yan APC,su ma kusoshin babbar jam’iyyar adawa ta PDP na gudanar da nasu tarukan inda suka ce ba za su yi kasa a gwiwa ba.
Yanzu dai lokaci ne kawai ke iya tabbatar da yadda za ta kaya a zaben gwamnan.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola: