Dan Takarar Kungiyar Hamayya A Nijar Ya Bayyana Shakku Kan Tsarin Zabe

Taron gangamin gamqyyar jam'iyun ADR na tsohon shugaban kasar Nijer Mahaman Usman

Tsohon shugaban kasar Nijer dan takarar gamayyar jam’iyun adawa na ADR a zaben shugaban kasa na 2021 Alhaji Mahamam Usman ya nuna fargaba dangane da tsare tasren zabubukan dake tafe saboda haka ya bukaci ‘yan kasar su tashi tsaye don murkushe dukkan wani magudin zabe.

Tsohon shugaban kasar da ya jagorantar wani gangamin magoya bayan gamayyar jam’iyun adawana dake matsayin dan takarar wadanan jam’iyu ya nuna shakku a game da tsare tsaren zabubukan 2020 da 2021 a bisa la’akari da yadda dan takarar jam’iyar PNDS TARAYYA mai mulki Bazoum Mohammed ke ci gaba da rike mukaminsa na minstan cikin gida, banda batun kwangilar hada kundin rajista da aka baiwa wani kamfani cikin yanayi mai cike da hazo inji shi…

Alhaji Mahamam Usman ya gargadi magoya bayansa da ma daukacin ‘yan Nijer su tashi tsaye don takawa masu mulki burki a yunkurinsu na maimaita abinda ya kira magudin da ya dabaibaye zabubuakn 2016 kuma a cewarsa aika Gandou Zakara mamba a kwamitin zartarwar jam’iyar PNDS domin shiga sahun alkalan kotun tsarin mulki alama ce dake gaskanta wannan zargi..

Shugaban kawancen jam’iyun FPR Ibrahim Yakuba dake cikin ‘yan siyasar da suka halarci gangamin na gamayyar ADR ya yi na’am da kiran na takwaransa .

Da yake maida martani akan wadanan zarge zarge na ‘yan adawa sakataren watsa labaran jam’iyar PNDS mai mulki Asumana Mahamadu ya yi watsi da zarge zargen da cewa soki burutsu ne kawai.

Wannan dambarwa na zuwa ne a wani lokacin da ya rage watanni 10 a je zaben kananan hukumomi yayinda zagayen farko na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin zai gudana nan da watanni 22 masu zuwa.

Saurari cikakken rahoton Souley Mummuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Dambarwar siyasa a Jamhuriyar Nijar-3:00"