Janaral Mohammadu Buhari, dan takarar shugaba na jam'iyar APC ta masu hamaiya yace, shi bashi da wani shaku gameda yin zabe a Nigeria. Janaral Buhari yayi wannan furuci ne daga London da wata hira da sashen Hausa yayi dashi.
Yace idan dai ba canji mulki zasu yi ba, in dai za'a bi ka'idodin kundin tsarin mulkin Nigeria, ba makawa dole su yi wannan zabe. Yace makon shiddan da aka kara, hukumar zabe ta kure malejinta, idan suka daga sun yi canjin mulki, wannan kuma tsakanin su da sauran 'yan Nigeria, inji Buhari.
Haka kuma Janaral Buhari yayi magana akan ikirarin da shugaba Jonathan na Nigeria yayi cewa, za'a kama Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram. Yace ai jam'iyarsa ta bada amsa akan wannan ikirari. A baya gwamnatin Nigeria tace an kashe Shekau, yaya kuma za'a yi suke Shekau yana da rai yanzu.
Akan zargin da gwamnatin Nigeria tayi cewa Buhari ne ke daurewa Shekau gindi, idan ta kama shi zai fadi haka. Buhari yace yana jiransu.
Your browser doesn’t support HTML5