Hukumar JAMB ta bada sanarwar cewa ta sayar da takardun rajistar zana jarabawar shiga jami’a kusan miliyan daya da dubu dari shida, yayin da ya rage saura kwanaki biyu a rufe sayar da takardun zana jarabawar shiga jami’o’i.
A yau juma’a ne shugaban bangaren yada labarai na hukumar Dr Fabian Benjamin, ya bayyana haka yayin da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a jihar Legas.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana cewa hukumar jarabawar ta fara sayar da takardun jarabawar neman gurbin karatu a jami’io’in ne a ranar 6, ga watan Disambar shekarar data gabata, kuma ta rufe sayar da takardun a ranan a ranar 6, ga watan Fabarairun wannan shekarar.
Ko da shike a ranar 6 ga watan Fabarairu, babban rajistiran hukumar Prof Ishaq Oloyode, ya bayyana kara wa’adin sayar da takardun zuwa ranar 11, ga watan na Fabarairu, a wani yunkuri na ba daliban da suka zana jarabawar amma basu sami nasara ba damar sake shiga cikin watannin biyu.
Mujallar Daily Trust, ta wallafa cewa Mr Benjamin ya ce rajistar jarabawar ta wannan shekarar da daya daga cikin wanda ya fi na kowanne lokaci tsaruwa da kyau.