WASHINGTON, D.C. - Yemi Mobolade yayi nasarar lashe zaben kujerar magajin gari, inda ya kasance bakar fata na farko da zai dare mukamin a Colorado Springs, birni na biyu mafi girma a jihar Colorado ta kasar Amurka da ke da tarihin kasancewa tungar masu ra'ayin mazan jiya.
Wannan nasarar ta Mobolade, dan gudun hijira daga Najeriya, kuma hamshakin dan kasuwa da bai taba rike wani zababben mukami a baya ba, shi ne koma bayan siyasa na baya-bayan nan ga jam’iyyar Republican a jihar da ta kasance jiha mai fada a ji.
Mobolade, wanda ya sami amincewar wasu fitattun 'yan jam'iyyar Republican, ya mayar da hankali kan batutuwa kamar daukar karin jami'an 'yan sanda, samar da gidaje masu saukin kudi, adana ruwa da magance matsalolin samun ayyukan kasuwanci.
Mobolade, mahaifin yara ƙanana uku wanda da ke auren wata ma’aikaciyar jinya, ya yiwo kaura daga Najeriya zuwa birnin da ke da yawan jama'a kusan 485,000 da aka sani da sansanonin soji da kuma kasancewa cibiyar Kiristanci na Ikklesiyoyin bishara inda ya fara kafa majami'a tsawon fiye da shekaru goma da suka wuce, kuma ya bude gidan sayar da abinci.
Ya kuma yi aiki a cikin gwamnatin birni a bangaren inganta ci gaban tattalin arziki da kuma taimakawa masu kananan sana'o'i.
Shi ne zai kasance magajin gari na farko wanda ba dan jam’iyyar Republican ba tun bayan da birnin ya fara zaben kantomomi shekaru 45 da suka gabata, a cewar jaridar The Gazette.
-AP