Matasa 80,000 ne daga Najeriya suka shiga wani shiri da Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ya dauki nauyi na kirkirar wata fasaha kan annobar COVID-19 da za a samar da mafita ga al'umma akan cutar, da suka kira “UNICEF COVID-19 Innovation Challenge”. Wadanda suka samu lambobin yabo daga Najeriya sun fara daga 'yan shekara 14 zuwa 35.
Daya daga cikin matasan mai suna Chukwuma Nwachukwu dan shekaru 28, ya gabatar da yadda za a yi amfani da hasken rana don samar da ruwa don taimakawa wajen yaki da kwayar cutar.
Fanfon da ya ke amfani da haken rana da Chukwuma Nwachukwu ya kirikira ya yi nasara a makon farko na fara gasar.
Chukwuma Nwachukwu ya ce, burin sa shi ne samar da tsaftataccen ruwan sha ga al'ummomin garin Abuja da ba su da damar samun ruwa mai tsafta.
Nwachukwu yana cikin dubbun matasa 'yan Najeriya da suka shiga shirin “UNICEF COVID-19 Innovation Challenge” wanda aka kaddamar a watan Mayu, aka kuma ci gaba har tsawon makonni shida.
UNICEF ta ce, sabbin kirkire-kirkiren sun nuna yadda matasa za su iya bayar da tasu gudummawa sosai lokacin da aka shiga mawuyacin lokaci.
Kimanin ‘yan Nigeria miliyan 60 ne, ko kusan kashi daya bisa uku na yawan ‘yan kasar, ba sa samun tsaftataccen ruwan sha, a cewar Hukumar ba da tallafni ruwan sha.