Rundunar ‘yan sandan jihar Neja a Najeriya ta ce ta na gudanar da bincike akan wani gida a unguwar gwari da ke cikin garin Suleja a jihar Neja, bayan da aka gano ana azabtar da yara a gidan.
Bayanai sun nuna cewa yaran su 15 ‘yan kasa da shekaru 10, wasunsu suna daure cikin mari kuma an ga alamun duka na bulala a jikinsu. Yaran dai an kai su wannan gidan ne domin yin almajiranci, al’amarin da ya sa ‘yan sanda ke rike da malamin mai suna Umar Ahmad Dan Shekaru 46, wanda ya sheda wa Muryar Amurka cewa ya daure yaran ne tare da azabtar da su saboda ba sa zama wuri daya. Ya kuma ce ba da niyar cutar da su ya yi haka ba.
Kakakin ‘yan sandan jihar ASP Wasiu Abiodun, ya ce sun damka yaran a hannun hukumar kare hakkin yara a jihar Neja domin duba lafiyarsu, sannan suna ci gaba da bincike domin gano gidan ko na haya ne ko kuma na Malamin ne, bukatar dai ita ce su gano abinda dokar kasa ta ce akan matsayin makarantar almajirai a wannan wuri,
Daraktar Ma’aikatar kula da hakkin yara a jihar Neja barista Maryam Kolo, ta ce yaran na samun kulawa ta musamman bisa la’akari da yadda suke cikin yanayi na yunwa da rashin lafiya da kuma ban tausayi. Ta kuma ce suna kokarin gano iyayen yaran kuma za su gabatar da su a gaban hukuma.
Bayanai dai sun nuna cewa yaran ‘yan asalin karamar hukumar Kacha ne da ke cikin jihar Neja.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum