Firayim Ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya fada a jiya Laraba cewa, an cimma gurin shekarar farko na cika babbar madatsar ruwa da ake ginawa a kogin Nilu, da ake takaddama a kai.
Madatsar ruwan ta Grand Ethiopia Renaissance Dam (GERD) da za a gina a kan kudi dala biliyan 4.6, za ta zama irinta mafi girma a nahiyar Afirka. Wadda za ta samar da wutar lantarki mai karfi a shekarar 2023, ana kyautata zaton, madatsar za ta samar da wutar lantarki mai karfin ma’aunin megawatts 6,0000.
“Mun sami nasarar kammala cika madatsar ruwa ba tare da cutar da kowa ba. A yanzu haka, madatsar ruwa ta cika makil," a cewar Ahmed a cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da shugabannin kasashen Habasha, Misira da Sudan suka hadu a wani taron koli ta yanar gizo, inda suka amince da fara tattaunawa game da madatsar ruwan.
Facebook Forum