Gwamnatin Saudiya ta haramtawa Salah dan kasa biyu da suka hada da Amurka da Saudi Arabia, har sai farkon wannan mako da ta dage haramcin. Dage masa takunkumin tafiyar ya biyo bayan wasu hotunan dake nuna yana gaisawar hannu da Sarki Salman da yarima mai jiran gado a ranar Talata. Labaran CNN ya fada a jiya Juma’a cewa ya iso Amurka amma dai ba a bayyana inda yake ba.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka da sakataren harkokin wajen Mike Pompeo Amurkan sun nuna farin cikin da dage wannan takunkumin tafiyar. Pompeo dai ya yi kira ga hukumomin Saudiya su baiwa Sala Kashoogi dama ya bar kasar.
A hali da ake ciki kuma kamfanin dillancin labaran Turkiya, yace kasar Turkiya ta bukaci Saudi Arabia ta mika mata mutane 18 da ta kama dangane da kashe dan jaridar nan domin yi musu shari’a a Turkiya.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga Saudi Arbia a jiya Juma’a da ta nuna inda gawar Kashoogi take da kuma ‘yan Turkiyar da aka gano sune suka yar da gawar bayan an kashe shi a ofishin jakadancinta a Istanbul.