Yansanda da lauyan mutumin nan dan kasar Nowe da ya amsa laifin kai harin bom a Oslo da kuma bude wuta a wani sansanin matasa sun bayyana yau lahadi cewa, yace shi kadai ne ke da alhakin kai harin, duk da yake wadansu shaidu sun ce akwai dan bindiga na biyu. Hukumomi sun ce Anders Behring Breivik ya amsa laifin kai tagwayen hare haren, sai dai ya musanta aikata laifi, da cewa, ko da yake hare haren da suka yi sanadin mutuwar mutaen 92 sun yi muni, duk da haka ya zama dole. babban jami’in ‘yansanda Oslo mai rikon gado Sveinung Sponheim ya shaidawa wani taron manema labarai yau lahadi cewa, babu wani mutum kuma da ake kyautata zaton yana da hannu a kai hare haren, sai dai hukumomi zasu bincike duk abinda Brevik ya fada. Ana tuhumar Breivik da aikata ta’addanci za a kuma gurfanar da shi gaban kotu gobe Litinin.
Yansanda da lauyan mutumin nan dan kasar Nowe da ya amsa laifin kai harin bom a Oslo da kuma bude wuta a wani sansanin matasa sun bayyana yau lahadi cewa, yace shi kadai ne ke da alhakin kai harin, duk da yake wadansu shaidu sun ce akwai dan bindiga na biyu.