Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta bayyana yau lahadi cewa, Kim Kye Gwan, mataimakin minista, kuma tsohon wakilin Koriya ta arewa kan batun ayyukan nukiliya zai kai ziyara a birnin New York wannan makon domin ganawa da manyan jami’an Amurka. Clinton tace, Kim zai gana da tawagar jami’an cibiyoyin Amurka domin tattaunawa kan matakan da ya kamata a dauka na komawa teburin tattaunawar da ta kunshi kasashe shida, da suka hada da koriyawan biyu da Amurka da China da Japan da kuma Rasha. Sakatariya Clinton ta bayyana cewa, ko da shike kofar Washington a bude take ta tattaunawa da Koriya ta arewa, bata da sha’awar wata doguwar tattaunawar da zata maida hannun agogo baya.
Jami'in Diplomasiyan Koriya ta arewa zai kawo ziyara Amurka domin tattaunawa kan batun nukiliya
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta bayyana yau lahadi cewa, Kim Kye Gwan, mataimakin minister, kuma tsohon wakilin Koriya ta arewa kan batun ayyukan nukiliya zai kai ziyara a birnin NY wannan makon domin ganawa da manyan jami’an Amurka.