A jiya Lahadi, masu aikin ceto na gaggawa a gabashin China suka samu nasara ceton wani dan karamin yaro daga buraguzon jirgin kasa mai shegen gudu, kusan sa’o’i ashirin da daya, bayan hatsarin da jirgin yayi, wanda ya kashe akalla mutane talatin da biyar da raunana fiye da mutane maitan a kudancin Shanghai. An dai ceci wanna yaro dan shekara hudu, ne bayan da tsawa ta apkawa wannan jirgin kasa daya taso daga birnin Hangzhou zuwa birnin Wenzhau akan wata gada sai kuma wani jirgin shima, mai dan karen gudu daya taso da birnin Fuzhou zuwa birnin Beijing yayi karo da jirgin da tsawa ta yiwa barna.
A jiya lahadin, mataimakin Primiyan China Zhang Dejiang ya ziyarci inda hatsarin ya auku, yayi kira ga shugabanin kananan hukumomin yankin da su agazawa wadanda hatsarin ya yiwa barna. A yayin ziyarar Mr Dejiang ya fada cewa, Majalisar Ministocin kasar ta kafa wani kwamitin da zai binciki musabbain hatsarin.
Kamfanin dilancin labarun kasar Xinhua ya ambace shi yana fadin cewa masu bincike zasu gano dalilin hatsarin, kuma za’a hukunta dukkan wadanda aka samu da laifin kamar yadda dokokin kasar suka tanada. Tuni har an kori wasu manyan jami’an hukumar safarar jiragen kasa ta Shanghai su uku.