Da farko fadar White House tace gwaji ya nuna bashi da cutar, bayan an gwada shi da iyayensa inda aka tabbatar da iyayen sun harbu a farkon wannan wata.
Uwargidan shugaban kasa ta fada a jiya Laraba cewa gwajin da aka gudanar a kan Barron da farko ya nuna bashi dauke da cutar sai dai daga baya da aka sake gwada shi sai aka tarar shi ma ya kamu da cutar COVID-19 da coronavirus ke haddasawa.
Gwajin da aka gudanar na baya bayan nan ya nuna Baron bashi dauke da cutar kamar yadda gwajin na iyayensa ya nuna.
Tun bayan da ita da shugaban kasa suka kamu da cutar a ranar daya ga watan Oktoba, ta rubuta cewa “hankalina ya koma kan dan mu.”
shugaban-amurka-trump-da-uwargidansa-sun-kamu-da-coronavirus
buhari-ya-yi-wa-trump-da-melania-fatan-samun-sauki
coronavirus-shugaba-trump-yana-jinya-a-asibiti
A cikin wani dogon bayani da aka kafa a yanar gizo, Malania Trump ta ce, “abinda na ke fargaba ya tabbata lokacin da aka sake gwada shi aka kuma tarar yana dauke da cutar.”
Ta bayyana cewa Barron matashi ne mai karfin zuciya wanda bai nuna wata alamar cutar ba. Kamar shugaba Trump, uwargidan shugaban kasar ta ce ta ji dadi da dukansu uku suka kamu da cutar a lokaci daya yadda zasu iya kulawa, da jinyar juna, su kuma dauki lokaci suna tare.
Uwargidan shugaban kasar tana kyakkyawan kare danta daga idon jama’a. Bata kuma bayyana dalilin da ya sa ba a sanar da lokacin da aka tarar ya kamu da cutar ba sai bayanda ya warke.