Dalilin Tura Dakaru Na Musamman Zuwa Kaduna

Wani jirgin yakin sama na Najeriya

Sanarwar ta kara da cewa, wannan karin dakaru, za su tallafawa jirage masu saukar ungulu biyu da aka tura domin tattara bayanan sirri.

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta tura dakarunta na musamman zuwa Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar domin su kara tallafawa tsaro a jihar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ta ce a ranar Lahadi aka tura dakarun, da zimmar dakile hare-haren da ake samu a wasu yankunan jihar.

Sanarwar ta kara da cewa, wannan karin dakaru, za su tallafawa jirage masu saukar ungulu biyu da aka tura domin tattara bayanan sirri.

Wadannan jirage a cewar rundunar ta sojin sama, suna ta sintiri a yankunan da aka fi samun tashin hankali kamar yadda jaridun kasar da dama suka ruwaito.

Jihar Kaduna ta sha fama da rikici mai nasaba da addini da kablianci a 'yan kwanakin nan inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

Yanzu wasu yankunan jihar na karkashin dokar hana zirga zirga.