Dalilin Da Ya Sa Na Kashe Hanifa – Abdulmalik Tanko

Marigayiya Hanifa (Instagram)

A ranar 4 ga watan Disambar 2021, Tanko ya yi garkuwa da Hanifa inda ya kai ta gidansa ya ajiye ta har tsawon mako biyu kafin daga bisani ya kashe ta.

Mai makarantar Noble Kids Comprehensive School, Abdulmalik Tanko, ya ce ya yanke shawarar kashe dalibarsa Hanifa Abubakar ‘yar shekara biyar ne bayan da ya yi tsammanin an gano yana garkuwa da ita a gidansa.

A ranar 4 ga watan Disambar 2021, Tanko ya yi garkuwa da Hanifa inda ya kai ta gidansa ya ajiye ta har tsawon mako biyu kafin daga bisani ya kashe ta.

“Ta zauna a gidana tare da iyalina tsawon kusan sati biyu. Akwai lokacin da malaman makarantarmu suka zo gidan sai nake tsammanin an turo su ne su bincika ko a gidan nawa take, saboda an ce yarinyar ta ambaci sunan uncle dinsu a wancan lokacin. Hakan ya sa na rasa mafita, a karshe na ba ta maganin bera.” Tanko ya fadawa jami’an ‘yan sandan jihar Kano.

Ku Duba Wannan Ma Hanifa: Abinda Mai Yiwuwa Ba Ku Sani Ba Daga Bakin Mahaifiyarta

Dan shekara 34, Tanko ya fadawa ‘yan sandan na Kano cewa da ya kashe Hanifa sai ya je ya sa daya daga cikin hadimansa a makarantarsu ya tona rami inda ya binne ta a farfajiyar makarantar.

Malamin ya kara da cewa ya nemi iyayen Hanifa da su biya naira miliyan shida a matsayin kudin fansa bayan da ya yi garkuwa da ita.

Tun dai da ta bata a farkon watan Disamba, hotunan Hanifa suka karade shafukan sada zumunta inda aka yi ta yekuwar neman inda take.

Sama da wata daya bayan sace ta, aka gano malaminsu ne ya yi garkuwa da ita, lamarin da shi ma kan ka ce kobo ya karade shafukan sada zumunta cikin dan kankanin lokaci.