Rahotanni daga Najeriya na cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarnin a rika karanta alkawarin nuna biyayya ga kasa (National Pledge) bayan rera taken kasa a taruka.
Tinubu ya ba da wannan umarni ne a cewar rahotanni yayin kaddamar da aikin gina rukunin gidaje 3,112 a yankin Karsana da ke Abuja, babban birnin kasar a ranar Alhamis.
“Dalilin farfado da wannan al’ada ta karanta alkawarin nuna biyayya shi ne don mu kara cusa akidar daraja kasarmu da nuna kishi.” Tinubu ya ce.
A cewar shugaban na Najeriya, za a rika karanta wannan alkawari a tarukan gwamnati da sauran taruka da jama’a suka shirya.
“Kafin na fito daga gida da safiyar yau (Alhamis,) na sa an buga min wannan alkwari na nuna biyayya, saboda ina so mu farfado da wannan akida a wannan taro.” Tinubu ya ce.
Tinubu ya yi nuni da nasarar da Najeriya ta samu akan kasar Afirka ta Kudu a gasar AFCON yana mai cewa, “mun gani jiya (Laraba) a filin wasa” yadda Najeriya ta samu nasarar da kowa ya yi ta nuna farin ciki – abin da ke nuni da kishin kasa.
Iya rera taken kasa (National Anthem) da karanta alkawarin nuna biyayya ga kasa (National Pledge,) batu ne da aka jima ana muhawara akai a Najeriya.
A baya, wasu rahotanni sun nuna cewa akwai manyan jami’an gwamnati da dama da ba su iya rera taken na kasa da kuma alkawarin nuna biyayya ba.